Wasu Daga Cikin Dalilan Da Ke Sa Bakin Haure Bullo Da Sabuwar Barauniyar Hanya Ta Hamada

Kamar yadda rahotanni suka bayyana rasuwar mutane 34 da kishin ruwa ya halla a hamadar jamhuriyar Nijar yayin da suke kokarin ketarawa zuwa kasar Algeriya.

A washegarin bayyanar labarin tsintuwar gawawakin mutane ne a arewacin jamhuriyar nijer masu bin diddigi akan al’amuran da suka shafi tafiye tafiyen ‘yan ci ranin nahiyar Afirka sun bayyana cewa tsauraran matakan tsaron da aka dauka akan hanyar Agadez zuwa Algeria sune dalilan dake sanya bakin haure kokarin bullo da sabuwar barauniyar hanya.

Ta dalili haka ne suka gargadi gwamnatocin kasashen Afirka ta yamma cewar su kara matsa kaimi a aiyukan fadakarwa da samarda ayyukan yi domin takaita wannan matsala dake daukar sabon salo a kulliyaumin.

Wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Sule Mumuni Barma ya tantauna da Saidu Abdu wani wanda ya gudanar da bincike akan dalilan yawaitar ‘yan ci ranin afirka kamar yadda zaku ji a wannan rahoton.

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu Daga Cikin Dalilan Da Ke Sa Bakin Haure Bullo Da Saubuwar Barauniyar Hanya Ta Hamada 3 '02"