Masana kimiyya da fasaha a kasar Amurka da Birtaniya, sun samu nasarar gano karin wasu taurari hudu, wanda kadan suka fi girman duniya, wanda mutun na iya ganin hasken su da kwayar ido.
Yin amfani da fasaha mai mahimmanci wanda zai iya auna ƙananan canje-canje a cikin hasken da wasu taurari sukan fitar, masana kimiyya a Jami'ar California Santa Cruz, da na Jami'ar Hertfordshire, sun gano taurari a kusa da tauraron Tau Ceti, wanda shine tauraro da ya kwashe tsawon shekaru 12, yana bada haske zuwa wannan duniyar.
Biyu daga cikin taurarin sararin samaniya, a yankin da ake kira wurin zama, suna nuni da cewar ana iya samun ruwa masu zurfi. Canje-canje da ake samu cikin haske, yana haifar da motsawa daga cikin taurari ko yin amfani da tauraro.
A kudancin gefen tauraron nan Cetus, yakan fitar da haske kamar da rana tsaka, wanda yake da kusan kashi 25 cikin dari na hasken da akan samu a sararrin sama a kowane dare.
Tsakanin taurari biyu a yankin wadanda girman su yafi girma fiye da duniya, suna rayuwar su ta dai-dai da dai-dai, duk dai da cewar masana rayuwar taurari na damun su, wanda hakan yake takurama rayuwar taurarin matuka.