WASHINGTON, DC —
Wata kotu a kaduna ta yankewa wasu matasa biyu Abdullahi Aliyu mai shekaru ashirin da takwas da Nura Ibrahim, mai shekaru ashirin da ukku, duk mazauna Unguwar Sahu Kaduna, hukuncin daurin shekara daya agidan yari da bulala goma kowane.
Wannan hukunci dai ya biyo bayan samun su da laifin satar wayar wutar lantarki mallakar hukumar wutar ta Kaduna, ne a tashar samar da wutar lantarkin hukumar dake Unguwar Abakwa, a Kaduna.
A makon da ya gabata ne wadannan matasa suka shiga harabar hukumar samarda wutar lantarkin suka yin awon gaba da wayar wutar lantarki.
Kakakin hukumar wutar lantarkin AbdulazeezAbdullahi, yace sun gamsu da hukuncin kotun da fatan zai kasance darasi.
Yanke hukuncin ke da wuya sai aka kwashe masu laifin zuwa gidan yari.