Wasu Sun Saci Warin Takalma Kafar Dama

Wani takalmi kafar hagu

“Wannan sun saka rayuwarsu ne cikin hadarin rasa ‘yancinsu na walwala akan warin takalmi daya da ba zai amfane su ba.”

Hausawa dai kan ce, “in da ranka, babu abin da ba za ka gani ba”. Wasu barayi sun shiga wani shagon sayar da kaya a jihar Virginia da ke Amurka suka saci takalma.

Amma abin da ya fi daure kan mai shagon da kuma al’umar yankin Roanake a jihar ta Virginia shi ne, kafufuwan dama kawai suka sace.

Da ma dai, Rob Wickham, mai shagon na takalma, ya kan ajiye kafufuwan dama ne a fili, da tunanin cewa idan barayi sun shiga shagon ba za su dauki wari daya ba kawai.

Ku Duba Wannan Ma Alakar Mata Masu Shaye-shaye Da Samartaka

Akalla wari takalma kafar hagu 13 barayin suka sace a tsakanin ranakun 20 ga watan Yuli da 25 ga watan Agusta, a cewar jaridar Express.

“Wannan sun saka rayuwarsu ne cikin hadarin rasa ‘yancinsu na walwala akan warin takalmi daya da ba zai amfane su ba.”

Tuni dai ‘yan san jihar ta Virgnia suka bayyana cewa suna tuhumar mutum guda da aika wannan laifi.