WASHINGTON, DC —
Babban kotun mai zama a Legas, ta yankewa dan wani basarake a jihar Legas, da wasu wa da kaninsa hukuncin kisa ta hanyar rataye su.
Mutanen ukku, Ibrahim Omilade, dan basaraken da Shola Oni da Kayode Oni, wadannan mutane dai sun yi sanadiyar mutuwar wani Suleiman Afolabi, ne wanda suka sassareshi da adda, a lokacin da suke fada dashi a ranar Kristimetin shekarar 2012, a unguwar Oshodi a Legas.
Mai shara’a Kudirat Jose, wace ta zartar da hukuncin, tace ta dogara da shaidar da aka gabatar a kotun.
A lokacin da take gabatar da hukuncin mai shara’a Kudirat, ta ja kunnen matasa cewa tana fata wannan zai kasance darasi a garesu, da fatan zasu guji sare saren mutane.