A birnin kwanni cikin jahar Tawa jamhuriyar Nijar aka gudanar da bukin cika shekaru 25 da soma gudanar da ayyukan kungaiyar nan mai suna CAIRE INTERNATIONAL da Amurka ta bullo da ita, wadda aka fi sani da suna mata masu dabara.
Wannan kungiya tana tallafa wa mata wajan samun bashi, ko yaki da jahilci, kiwon dabbobi da noma da ayyukan raya kasa da kiwon lafiya domin yaki da fatara da talauci a cikin kasar da ke baya a jerin kasashen da hukumar majalisar dinkin duniya mai kula da harkokin bunkasa rayuwar al’uma ta jera.
A cewar gwamnan jahar Tawa da ya jagoranci bukin tare da magatakardar kundumar birnin Kwanni da sarakunan gargajiya da magadan gari da kuma sauran ma’aikata na jaha tare da mata manya da kanana da suka yi dandazo a wurin da aka gudanar da wannan buki cewa yayi wannan wani gagarumin abin alheri ne ga jama’a dama kasar baki daya.
A cewar shugabar ma’aikatar da ke daukar valhakin kula da ayyukan kungiyar a mataki na kasa Dr Fatima Zainu, wannan tsari yana taimaka wa maza da mata baki daya.
Malam Yahuza da ke wakiltar wata kungiya dake birnin kwanni cewa yayi wannan dabara ta mata masu dabara ta zagaye duniya domin kuwa a yanzu haka kusan sama da kasashe arba’in tsakanin Amurka da turai sun fara gudanar da irin wadannan ayyuka.
A yanzu haka dai sama da mata dubu goma sha biyar ne ke cin moriyar wannan shiri a jamhuriyar Nijar.
Ga rahoton Mamane Harouna daga jamhuriyar Nijar.