Ya Jefa Dansa Dan Shekaru 14 Cikin Rijiya

I

Wani mutun mai suna Papa Ogada, mai sana’ar akwatin daukar gawa a karamar hukumar Obingwa dake jihar Abia, ya jefa dansa dan shekaru 14, cikin rijiya domin yana zargin cewa dan nasa maye ne.

Rahotani na cewa Papa Ogada, yana korafen cewa dansa maye ne wanda kuma shi yake jawo masa matsalolin yaruwan da yake fuskanta tunda ya dawo wurinsa bayan da ya bar wurin mahaifiyarsa.

Papa Ogada, da taimakon wani abokinsa suka daure yaro da kayan makarantansa da littatafansa suka jefa shi a cikin mota zuwa kauyen Abiaka dake makwabtaka dasu da misalign kaefe 9.00pm. na dare inda suka jefa shi a cikin wata rijiyar ta ba’a amfani da ita.

Daga bisa sai yaro ya ci gaba da ihu wanda ya jawon hankalin mutane kauyen wadanda suka kawa masa dauki suka fito dashi daga rijiyar yanzu haka yaro na samu magani a wani asibiti, shi kuwa mahaifin yaro ya ranta a na kare.

Hukumoni ‘yan Sanda sun ce ba’a kawo masu rahotun ba amma yana iya faruwa ya kasance ba’a shedawa jami’an ‘yan sand aba.