Ya Kashe ‘Ya’Yan Sa Domin Yin Tsafi

Rundunar ‘yan Sandan birnin tarayya Abuja, ta cafke wani matashi Thomas Mathew, mai shekaru talatin da biyar, wanda ake zargi da kashe ‘ya’yan sa biyu domin yin tsafi.

Kwamishinan ‘yan Sandan Abuja, Muhammad Mustapha, wanda ya tabbatar da labarin ya ce wanda ake zargin Thomas Mathew, ya kashe ‘ya;\’yan biyu ne a bisa umarni mahaifisa.

Mathew, mazaunin Asokoro, ya ce mahaifinsa kafin rasuwar sa ya shigar da shi wata kungiya ta asiri, kuma acewarsa mahaifin nasa ya taho masa cikin mafarki ya umarce shi daya sadaukar masa da ‘ya’yan sa a lokuta daban daban.

Matar Mathew, mai suna Bola, tace hakan nan ya tsiri rigima ya fara dukanta sai ta nufi gidan yayarsa kafin su dawo da yayar tasa ya kule kofa sai suka nufi wurin ‘yan Sanda, daga bisani 'yan sanda suka balle kofar koda aka shiga dakin ya riga ya kashe ‘yarsu.

A lokacin da yake amsa tambayoyi Mathew, yace mahaifinsa yayi alkawarin zai maida shi mai arziki idan ya sadaukar masa da ‘ya’yan sa.