Ya Kawo Karshen Yajin Cin Abinci

Wani mawaki kuma dan gwagwarmaya Luady Beirao, dan kasar Angola, kawo karshen yajin cin abinci wanda ya kwashe kwanaki 36, yana yi bayan da Iyalai ‘yan uwa da abokan arziki suka roke shi daya dakatar da yajin cin abincin.

Wannanya biyo bayan tsoron da suke yi ne domin lafiyar sa, shi dai Beirao, da wasu ‘yan gwagwarmayan su goma sha hudu an tsaresu a gidan yarin Angola.

Su dai wadannan mutane na fuskatar laifin yiwa kasar zagon kasa ne bayan da aka kama su a watan Yuni, a lokacin da suke wani taron akan littafi.

Farfesa Melissa Moorman, na Jami’ar Indiana, a Amurka, ya shaidawa muryar Amurka cewa, mutanen na suna taron akan damokradiya da milkin kama karaya a lokacin da aka kama su.