Yau ne Najeriya ta cika shekaru 55 da samun 'yancin kai daga mulkin mallaka karkashin turawan Ingila, koda shike kasar ta fuskanci wasu kalubale da dama musamman ta wajan harkokin tattalin arziki da tsaro. Ibrahim Jarmai ya tattauna da wasu matasa ta wayar tarho inda suka bayyana ra'ayoyin su kamar haka;
Matashi Abbas Baffa Cheledi daga jahar Bauchi cewa yayi "a gaskiya mu dai a jahar Bauchi abin ba laifi, an sami ci gaba ta wajan harkar ilimi da sauran wasu bangarori sai dai muna bukatar gwamnati ta gyara mana wasu hanyoyi da kuma kara samar mana da ayyukan yi. Daga karshe yayi kira ga matasa da su mike su fara sana'a, su kuma nemi ilimi tunda a cewar sa, ga makarantu nan a ko ina."
Shikuma Muhammadu Shaffi'u a nasa ra'ayin cewa yayi " matasa su tashi domin yanzu zamanin zaman banza ya wuce, kuma ya kamata su sani cewa matasa sune ƙashin bayan duk wata al'uma. dan haka lallai ya zama dole ne matasa su kara azama."
Da muka waiwaya wajan nakasassu kuma, wakilin muryar Amurka Muhammada Ibrahim Kwari ya zanta da wasu inda suka fadi ra'ayoyin su akan irin ci gaban da aka samu a kasar daga lokacin da aka sami 'yancin kai.
Kodashike dayawa sun nuna rashin jin dadin su ne inda suka koka da cewar mahukuntar kasar sun mayar da su saniyar ware wajan tafiyar da al'amurran kasar.
A daya bangaren kuma, wasu nakasassun sun ce gaskiya kwalliya ta biya kudin sabulu sakamakon samun 'ya'yan talakwa a harkar siyasa da kuma fafatawa da ake da su a harkokin gwamnati.
Ga Karin Bayani.