Matasa a jihar Filato, sun dauki alkawarin gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali, da lumana batare da nuna banbancin kabila ko na addini ba.
Sun bayyana haka ne a wani taron da suka kira don wayar wa juna kai kan mahimmancin yin zabe batare da tashin hankalin ba, matasan sun kuma fadakar da juna da suyi zabe a bisa cancanta, da cewa a wannan karon ba zasu yarda ayi amfani dasu ba.
Daya daga cikin wadanda suka gabatar da kasidu, da yiwa matasan hudubar zaman lafiya, Darakta, a cibiyar inganta ci gaban al’uma, Mr. Tony Garba, yace matasa sune kashi saba’in na al’uma, don haka dole ne suyi kishin kasar su fiye da kowane mutun.
Mr. Tony Garba Ya kara da cewa “ Tunanin kasar mu shine zai zama na farko, muna neman ci gaban kasar mu ne, muna neman zaman lafiya na kasa, muna so matasa su samu aiki, muna so abinci ya bunkasa, yayi da zaka je ka jefa kuri’a, a zuciyar ka da yardar Allah, ka san mutumin da idan aka bashi wannan wurin za rike da amana, amma idan kaje ka jefa kuri’a, saboda cewa addini mu daya ne, ko kuma kabilar mu daya ne toh babu mamaki gobe idan mutumi nan ya shiga bazai waiwaye ka ba, saboda shi ya shigo, akan wani dalili, wanda ya wuci yazo ya taimaki talakawa, yayi masu aiki, saboda haka babban shawara ga matasa, a wannan lokaci shine yayin da zamu je mu jefa kuri’ar mu, muyi tunanin Najeriya, duk, shugaban da zamu bashi kuri’a, mu tabbatar har ga Allah, cewa zai rike amana.”
Shi kuwa wanda ya kirkiro da shirin wayar da kan matasan Aminu Hussaini, yace amfanin demokradiya, shine a hada mata da maza da matasa a harkokin gudanar da mulki don samun ci gaba mai inganci a Najeriya.
Ya kara da cewa wannan taro ne don zaben dake tafe kuma yakamata mu gayawa kanmu gaskiya, muga kuma yadda zamu hada kai muyi zabe a bisa akida nagari, matasa daga addinai da kabilu daban-daban ne suka halarci taron.
Your browser doesn’t support HTML5