Yaki da Jahilci na Magance Matsalolin Yau da Kullun

Matashi Mai Sana'a da Yaki da Jahilci

Babu abun da yafi ilimi dadi a rayuwar yau da kullun, zama mai ilimi shine wani abu da babu wanda zai iya kwace maka, kuma zama mai ilimi shine wani abu da zai ba mutun damar iya mu’amala da mutane a kowane irin hali.

Shi ilimi ginshikin zaman duniya ne, wanda ta hakan mutun na iya zama komai a rayuwa, don haka yakamata ace kowane irin mahaluki ya dukufa wajen neman ilimin yau da gobe, don cin ribar zaman duniya.

Wannan wani kirane da wani bawan Allah me suna Sani Mustapha, daga Shagari kwatas, yayi wanda yake kasuwanci kuma yana neman ilimi ta hanyar yaki da jahilci, kasancewar baiyi karatun boko ba na shiga aji, amma yanzu da girmanshi ya koma makaranta don fahimtar rayuwar yau da kullun, don ya fahimci sai kana da ilimi zaka iyayin komai a rayuwa.

Don idan mutun bashi da ilimi to zakaga cewar yasamu nakasu a gudanar da rayuwar shi, saboda ko kasuwanci mutun yakeyi to zakaga cewar wanda yake da ilimi yana gudanar da kasuwancin shi fiyeda wanda bai da ilimi.

A takaice dai zakaga cewar shi duk mutun mai ilimi yafita da ban da wanda bai da ilimi ko a harkar mu’amalar su ta yau da kullun.

Don haka a she yakamata matasa su tashi tsaye wajen neman ilimi don su samu su yi dai daito da zamani, da kuma iya tafiyar da kowace irin rayuwa a tsakanin al’umah.