'Yan Boko Haram Sun Sace Mata 60 Da Maza 30 A Borno

Wasu daga cikin daliban Chibok da suka kwace daga hannun Boko Haram

Wasu mayakan da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun sake satar mutane masu yawa a Jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, a yankin da aka sace dalibai mata su fiye da 200 a watan Afrilu.

Jami'an yanki da mazauna wasu kauyuka sun fada yau talata cewa 'yan bindigar sun sace mata su kimanin 60, manya da kanana, da kuma yara maza su fiye da 30, a hare-haren da suka kai kan wasu kauyuka kimanin kilomita 100 daga Maiduguri, babban birnin Jihar.

Suka ce 'yan bindigar sun kashe mutane kimanin 4 a lokacin wadannan hare-hare.

Wani jami'in hukumar tsaron cikin gida ta Najeri9ya, SSS, ya fadawa VOA Hausa cewa lallai an sace mutane a yankin. Amma kuma jami'in, wanda ba ya son a fadi sunansa, yace ba a tabbatar da yawan mutanen da aka sace ba.

babu dai wanda ya dauki alhakin satar mutanen amma jami'ai sun ce su na kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka aikata wannan ta'asar.