WASHINGTON D.C —
Da muka koma bangaren 'yan mata kuma, suma sun fada mana nasu ra'a yoyin inda yawancin su suka danganta lamarin da kwadayi, wasu kuma suka bayyana cewar ba maganar kwadayi bace illa shakuwa ko sabo.
Kamar yadda daya daga cikin 'yan matan ta bayyana ra'ayinta cewar lallai yawancin lokuta samarin kan nuna cewar suna kaunar su da zuciya guda wanda hakan kan sa 'yan matan su saki jiki da su amma daga bisani sai sun gama shakuwa sai dan'adam ya yi halinsa.
Yawancin lokuta dai 'yan mata kan dorawa samari laifi musamman idan hakan su bai cimma ruwa ba, ko yaya kuke ganin lamarin a naku tunanin?.
Tofa albarkacin bakin ka a shafin mu na facebook a dandalinvoafacebook.com domin bayyana ra'ayi da kuma tafka muhawara.