Yau Ce Ranar Wasanni Ta Duniya

Wasan Olympic

A kokarin samar da zaman lafiya da cigaban al’uma, wasanni tsakanin a’uma daban daban na da fa’ida kwarai musamman yadda ake samun Karin dankon zumunci a tsakanin kasashe da kabilu daban daban a duniya.

Majalisar dinkin duniya da kwamitin shirya wasan Olympic sun ware ranar 6 ga Afirilu, ta kowace shekara a matsayin ranar wasanni ta diniya. Makasudin wannan rana shine domin hadaka da kuma tallafawa kwamitin domin cigaban wasanni a duniya da kuma taimakawa kananan yara.

A wata hirar da wakiliyar sashin Hausa Baraka Bashir tayi, matasa da dama sun tofa albarkacin bakinsu akan muhimmancin wassani da kuma muhimmancin tsaida wannan rana a matsayin ranar wasanni ta duniya.

Majalisar dinkin duniya tace an zabi wannan rana ne saboda tayi daidai da ranar da aka fara wasannin guje guje da tsalle tsalle a duniya na Olympic a birnin Athens na kasar Girka a shekarar 1896.