A yau Litinin ake sa ran kamfanin Apple zai sanar da sabon tsarin shi na gidan talabijin. Tsarin da zai yi gogayya da sauran kamfanonin talabijin na yanar gizo kamar su Netflix, Amazon da kamfanin Cable TV.
Wannan shine tsarin da aka jima ana dakon fitowarsa, sabon tsarin na dauke da manhajar kallon talabijin kai tsaye, da wasu fina-finai. Kamfanin na Apple ya kashe fiye da dala billiyan $1.
A cikin tsarin akwai manhajojin da zasu ba mutun labaran duniya daga gidajen jaridu da dama, kana ana iya kallon wasannin kwalo kai tsaye, harma da karatun jaridu.
Tsarin dai zai ba mutane damar kallon duk wasu shirye shirye, da ake gudanarwa a wasu tashoshi, babu bukatar mutun yayi amfani da talabijin ko kwamfuta don kallo a duk lokacin da bukatar hakan tazo.