Yau Ranar Lafiya ta Duniya - 7/4/14

NAJERIYA - Yau take ranar lafiya ta duniya. Dr. Sani Garko na koyarwa a jami’ar Ahmadu Bello Dake Zariya “rana ce wadda ya kamata, wata kila a samu wani yanayin matsala ta rayuwa, ko ta lafiya a fuskance ta, saboda ko a wayar da kai, ko ayi wani yunkuri daga wajen gwamnati wanda zai taimaki mutane”.


NAJERIYA - Shin wani kwam gaba kwam baya PDP take hangowa yayin da zaben kananan hukumomi ke karatowa a jihar Kano? Malam Ibrahim Shekaru dan PDP ne “muna nan daram-dam, zamu shiga zabe PDP zata shiga zaben kanan hukumomi na jihar Kano. Baza mu ja da baya.


NAJERIYA - Yau kusan kwanaki bakwai kennan hukumomin Najeriya basu mayar mana da martani dangane da kalaman wani mutum da yace shi sojan Najeriya ne, kuma har ma yayi karin haske akan abubuwan dake wakana a bayan fage dangane da yaki kungiyar da aka fi sani da Boko Haram. Ya bayanna cewa akwai sojojin Najeriya a Boko Haram, kuma sansanin Boko Haram da dakarun Najeriya bai fi tazarar kilomita biyu tsaknainsu ba. Har yanzu sashen Hausa na Muryar Amurka na neman martanin hukumomin Najeriya.

Your browser doesn’t support HTML5

Labaran Najeriya - 4'00"