Za’a Fara Kera Kayayyakin Fasaha A Najeriya

Microsoft Design

Hukumar kula da habaka kayan fasaha na zamani ta Najeriya NITDA ta baiwa shahararren kamfanin nan na Afirka RLG takardar shaidar kera kayan fasaha a Najeriya, hakan na nufin RLG zai fara kera da hada kwamfitoci da wayoyin hannu da sauran kayan fasaha makamantansu.

A wani rahoto da jaridar Punch ta fitar ya nuna cewa kamfanin RLG ya fara neman takardar izinin daga NITDA tun a watan Afrilun shekara ta 2014. Tsawon shekara guda kenan bayan hukumar ta gama bincikenta da gwaje-gwajen ginin kamfanin kafin ta amince.

Daraktan hulda da jama’a na RLG dake kula da yammacin Afirka, Mr. Tosin Ilesanmi yace wannan takardar amincewar da kamfanin ya samu a Najeriya zai taimaka wajen ware kasar daga cikin kasashen da sai an kera ake kawo musu.

Har yanzu dai babu wani taka mai mai kan yadda kamfanin zai gudanar da aikin sa kuma wanne irin kayayyaki zai ke kerawa a najeriyar. Yawancin kamfanonin da sukayi yunkurin kera kayayyakin fasaha dana sadarwa na zamani a nahiyar Afirka, an dai sansu da kera ire-iren kayayyakin a kasar China.

Kamfanin dai yaki yin bayani kan tambayar da akayi kan irin kayayyakin da zasu ke kerawa, kamfanin dai ya kafu tun shekara ta 2001, a kasar Ghana yana kuma kera kwamfutoci da wayoyin hannu da sauran kayan fasaha.