Za'a Kece Reni Tsakanin Najeriya Da Brazil

'Yan Kwallon U 17

A bayan da Golden Eaglets na Najeriya da takwarorinsu na kasashen Brazil, Mexico da Belgium suka haye zuwa ga wasannin kwata fainal a gasar cin kofin duniya ta samari ‘yan kasa da shekara 17 ran laraba a kasar Chile, sai a ran alhamis kuma Mali da Croatia da Ecuador da Costa Rica su ma suka samu damar lashe wasanninsu na zagaye na biyu, suka haye zuwa ga wasannin kwata fainal su ma.

Tun daga farkon wasa, kasashen Mali da Croatia da Ecuador suka mamaye wasanninsu amma ita kam Costa Rica sai da kyar ta kai labara a hannun ‘yan wasan kasar Faransa wadanda kafin wasan alhamis din suka rika zura kwallaye kamar ruwan sama.

‘Yan wasan Faransa sun mamaye wannan wasa daga farkonsa har karshe, amma suka kasa jefa kwallo cikin ragar ‘yan Costa Rica, karshenta sai da aka je ga bugun fenariti inda CRC ta lashe da ci 5-3. Faransa tana daga cikin kasashen da aka sanya ma ran daukar wannan kofi tun farko.

Ecuador ta doke Rasha da ci 4-1, yayin da ‘yan wasan Croatia, wadanda su kadai ne kawai suka samu nasara kan ‘yan Golden Eaglets na Najeriya, amma a zagayen farko, suka doke Jamus da ci 2-0.

Mali kuwa, cikin sauki ta gama da ‘yan wasan KTA da ci 3-0.

Yanzu a ranar lahadi za a fara buga wasannin kwata fainal inda Najeriya zata kara da Brazil yayin da Mali zata gwabza da Croatia. A ranar litinin kuma, Ecuador zata kara da Mexico yayin da Belgium zata kece raini da CRC.