Zaben Najeriya Tana Kasa Tana Dabo

Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, (INEC) Attahiru Jega

Shugaban jam’iyyar PDM, Alhaji Bashir Yusuf, bayan fitowa daga dakin taro da shugaban hukumar zabe, inda yace su basu amince da dage zaben 14, ga watan nan ba.

A zahiri jam’iyun su rabe gida biyu, masu mara baya ga PDP, mai mulki suna cewa a jikirta ko kuwa a cema a dage zaben, ma’abota babba jam’iyyar, adawa ta APC, suna cewa a gudanar da zaben.

Mataimakin shugaban jam’iyyar, PDP, Uche Sekondos, ke cewa ba’a yi masu adalci ba idan an ce sun ce a dage zaben, manufarsu a duba lamuran tsaro a jinkirta zaben.

Your browser doesn’t support HTML5

Zaben Najeriya - 3'06"