Zama Da Madaukin Kanwa

Ibrahim Salo Mawaki

A shirin mu na nisahdi a yau dandali ya sami bakwanci mawaki Ibrahim Salo, wanda aka fi sani da IB Salo , ya ce ya fara waka sanadiyar bin wasu mawaka a garin Legas da suka hadar da Young Clip da sauransu kasancewar yana sha’awar harkan ne ma ya sa ya kasance ya na lura da yadda suke rubata waka da ma rera ta.

A shekara ta 2009 sai suka dawo garin kano inda a nan ma bata canza zane ba domin kuwa ya tsinci kansa kusa da wasu mawaka wanda ya hasassa cikan burinsa.

IB Salo, dai ya ce yana rubuta wakokin mussamam na soyayya, ko da ya ke ya ce abin sha’awa a harkar wakar dai bai wuce yadda idan ya saurari rediyo ya ke jin ana kiran sunayen mawaka ,kuma mafi yawansu sun yi fice- toh shima IB Salo burinsa yayi fice.

A fannin tsegumi kuwa a jiya ne Shugaban Arewa film makers reshen jihar Kano Alhaji amilu Ahmad Yakasai da Ali Nuhu Adam Zango da sauransu suka sauka a kasar Burtaniya , domin karbar kambin karramawa a bikin karama jarumi na Africa films Award.