Zeenat Tanko: Sana'a Ta Kafar Yanar Gizo Na Kawo Alheri

Zeenat Lawal Tanko

Zeenat Lawal Tanko -- wata matashiya mai sana’ar hajja da suka danganci atamfofi, leshi da kuma kayan kicin na mata, inda ta ke amfani da shafin sadarwa na zamani domin tallata hajjarta.

Shekaru uku kenan da ta tsunduma tana wannan sana’ar, wanda ‘yar ta ce ta ja hankalinta wajen dogaro da kai, bayan ta kammala karatunta na digiri, ta hanyar ba ta kaya domin ta sayar ma ta daga baya sai ta bata kudaden kayan da ta sayar da haka ne ta fara sana’a.

Ta kara da cewar dukkanin cinikayya da ta kanyi suna afkuwa ne ta hanyar tallata su a shafin Whatsapp, ko Instagram, a yanzu har ta kai suna fitar da ashobi na buki duk a yunkurin dogaro da kai.

A yanzu haka Zeenat ta na yi wa kasa hidima, a hannu guda kuma tana sana’o'inta na dogaro da kai, a yunkuri taimakawa iyayenta ta hanyar daina tambayarsu kudi domin kashewa kanta bukatu.

A harka ta ta hajja a ta bakin Zeenat ta ce bata ba da bashi domin kuwa ko a kwanaki ta ce ta fuskanci kalubale inda wata ta bukaci da ta kawo mata ashobi, bayan ta hada kayan masu yawa sai matar ta ce an daga bukin, don haka sai ta barta da kaya.

Sai kasuwa ta kai ta karyar da kudaden kayan sannan ta maida kudinta, har ila yau ta ce ko tallata hajja ta shafin sadarwa ana samu wasu matsaloli da ba’a rasa ba inda wasu kan sace hotunan kayan da mutu ya saka domin tallata su a matsayin nasu.

Your browser doesn’t support HTML5

Zeenat Tanko: Sana'a Ta Kafar Yanar Gizo Na Kawo Alheri 5'20"