A yau Laraba ne shugaban kasar Amurka Barak Obama ya marabci Fafaroma Francis, shugaban darikar Katolika ta duniya, tare da dumbin Jama’a da yawansu zai kai dubu goma sha biyar a fadar White House.
Shugaban da matarsa Michelle Obama, sun kai gaisuwarsu ga Fafaroma a lokacin da ya isa fadar shugaban kasar.
A lokacin da ya ke bayani, shugaba Obama ya fada wa Fafaroma cewa farin cikin zuwansa Amurka da ake yi ba don Matsayinsa ba ne amma don irin kyawun halayensa.
A lokacin da Fafaroma ya yi nasa jawabin, ya fadi cewa burin ‘yan darikar Katolika da ke Amurka shi ne ganin sun gina al’ummar da zata mutunta kowa, a kuma zauna lafiya tare da kare hakkokin juna, da kuma kyamatar duk wani nau’in rashin adalchi da nuna bambanci.
Fapfroma kuma ya taba batun chanjin yanayi da a ke takaddama a kanshi, inda ya ce ya sami kwarin guywa sosai akan kokarin da shugaba Obama ke yi na kawas da matsalar gurbatacciyar iska.