Amurka ta yi Allah wadarai da harin bam na kunar bakin-waken da aka kai yau litinin kan daliban makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati dake garin Potiskum a Jihar Yoben Najeriya.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Jen Psaki, ta fada cikin wata sanarwa cewa Amurka tana mika ta'aziyya da jajenta ga 'yan'uwa da iyalan wadanda aka kashe ko aka jikkata a hari na baya-bayanan nan na tsagera da suka dukufa kan tayar da fitina da zub da jini a wannan yanki na arewa maso gabashin Najeriya.
Jen Psaki ta ce Amurka tana yin kira ga gwamnatin Najeriya da ta gaggauta farautowa da hukumta wadanda suka aikata wannan mummunan ta'addanci a kan fararen hular da ba su yi ma kowa komai ba.
Shi ma babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, yace ya harzuka matuka da yawan hare-hare da kuma tsananinsu a kan makarantu a yankin arewacin Najeriya.
Mutane akalla 48 ne aka tabbatar da mutuwarsu a harin bam da wani dan kunar bakin wake ya kai yau litinin da safiya a makarantar sakandaren ta Potiskum. Babu wanda ya dauki alhaki har yanzu, amma ana kyautata zaton wannan aikin kungiyar ta'addanci ta Boko Haram ce.