Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Dakatar Da Ibrahimovic


Dan wasan AC Milan, Zlatan Ibrahimovic, bayan da ya jefa kwallo a ragar 'yan Napoli, litinin 28 Fabrairu 2011
Dan wasan AC Milan, Zlatan Ibrahimovic, bayan da ya jefa kwallo a ragar 'yan Napoli, litinin 28 Fabrairu 2011

Hukumomin kwallon kafa na Faransa sun dakatar da dan wasan gaba na PSG, Zlatan Ibrahimovic, daga buga kwallo har na wasanni 4 a bayan da ya fito yana sukar lamirin alkalin wasa Lionel Jaffredo.

Ibrahimovic ya fito da kakkausar harshe yana caccakar alkalin wasa Jaffredo a bayan da kungiyar Bordeaux ta doke PSG a watan da ya shige.

Dan wasan dan kasar Sweden ya sake sanya kafar wando da hukumoimin kwallon kafar Faransa a bayan da aka ji shi, aka kuma gan shi a faifan bidiyo, yana yin Allah wadarai da alkalin wasa a lokacin da Bordeaux ta doke PSG da ci 3-2 a wasan Ligue 1.

Aka ce ma zage-zage yayi marasa dadi. Daga baya Ibrahimovic, wanda ya taba buga kwallo ma kungiyoyin FC Barcelona da Inter Milan, ya nemi gafarar subul da bakan, amma duk da haka bai kaucewa wannan hukumcin ba.

Wannan dakatarwar zata fara aiki daga ranar talata 14 ga watan nan, ma’ana, zai iya bugawa a wasan karshe na cin kofin Coupe de la Ligue da kungiyarsa ta PSG zata yi da Bastia gobe asabar.

XS
SM
MD
LG