Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kano Pillars Basu Da Wani Zabi


Tambarin Kano Pillars
Tambarin Kano Pillars

Zakarun ‘yan kwallon Najeriya na Kano Pillars basu da wani zabi yanzu illa komawa gida su sake tada komadar su, biyo bayan kasawa da cigaban zagaye na biyu na gasar cin kofin kulob kulob na Afirka CAF a karshen sati.

Pillars sun sha gagarumin kaye a zagayen na farkon wasansu da kulob din Morocco Moghreb Tetouan, a yanzu abinda ya rage masu shine kokarin kare matsayinsu a premier league.

“Zamu mayar da hankali akan gasar” a cewar mai bada shawarar kulob din Okey Emordi a hirar su da jaridar daily independent.

Emordi ya kuma kara da cewa “Zamu cigaba da horo da sake fasalin al’amura, a kasancewar iyali guda, akwai masu kyau da kuma marasa kyau. Zamu cigaba da aiki tukuru dan samun alfanu a wannan kakar da kuma nan gaba.”

Abubuwa da dama sun faru da tawagar ‘yan wasan a cikin satin nan. Bamuji dadin fita gasar a wannan matakin, munyi matukar son samun wani abu a wannan lokacin amma hakan bazai yiwuba.

Pillars sun rasa kwallon su ta farko yayin da ‘yan wasan Morocco suka yi masu ci 4 da babu.

“’yan wasan sunyi wasa mai kyau kuma naji dadin irin himmar da suka sa a baya hutun rabin lokaci a wasan da akayi a Kano, inda sunfara haka da farko da wasan ya kasance daban da haka” a cewar Emordi.

XS
SM
MD
LG