Shugaban magoya bayan kulab ‘din Kano Pillars Bashir Ma’azu Jide, ya nuna cewar fashi da makamin da akayi musu ya jefa kulab din cikin wani hali, kuma shine dalilin dayasa suka sha alwashin fitowa wasa da karfin mu cikin wannan ranin wasan.
Kano Pillars dai sun ci wasan da sukayi 2 – 0 a filin wasan Sani Abacha, amma bazai sa su huce haushin kashin da klub din Moghreb Tetouan, ya basu ba inda ya lashe wasan 4 – 0.
An dai kai wa ‘yan wasan Kano Pillar hari a Abaji kan hanyar Abuja - Lokoja, wanda aka harbi biyar daka cikin manyan ‘yan wasan su.
Ma’azu ya gayawa Goal cewa, “kamar yadda nake gani a gurina, na gamsu da kokarin da ‘yan wasan mu sukayi, kuma magoya bayan kungiyar sun bamu hadin kai da kwarin gwiwa.”
Yaci gaba da cewa tun harin da ‘yan fashi suka kai mana, mun rasa ‘yan wasan mu masu kyau. Idan aka duba yadda mukayi wasan, za’a ga bamu da ‘dan wasan gaba da tsakiya amma mun shirya ‘yan wasan da zasu rufe gabar. Muna tsammanin kulub ‘din zai dawo ya kara shiri da gyara kurakuran da mukayi. Gobe ma rana ce.