Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Didier Drogba Ya Ginawa Talakawa Asibiti


##caption Didier Drogba ##
##caption Didier Drogba ##

Mashahurin dan wasan tamaula na kasar Cote D’Ivoire, Didier Drogba, ya kaddamar da asibitin farko daga cikin asibitoci guda 5 da yayi alkawarin ginawa kyauta a kasar.

Wannan asibiti da aka gina a wata unguwa mai suna Attecoube dake Abidjan, a kan tsabar kudi dala miliyan daya ko Naira miliyan 200, zai fi maida hankali wajen kula da mata da yara marasa galihu.

Asibitin yana dauke da kayayyakin kiwon lafiya na zamani, ciki har da na’urorin ultrasound, da sashen kula da mata da yara, da na hoton x-ray, da dakin gwaje gwaje, da wurin bada magani da kuma dakunan kwantar da marasa lafiya wadanda ake kebewa saboda irin cututtukansu.

Ana sa ran wannan asibiti zai rika kula da marasa lafiya dubu 50 a kowace shekara.

Sauran asibitocin da Didier Drogba yake ginawa, ana yinsu ne a garuruwan Yamoussoukro, San Pedro, Man da kuma Korhogo. An ce nan da ‘yan watanni kadan za a kamala su.

A ranar 18 ga watan nan na Afrilu, Gidauniyar Didier Drogba zata gudanar da wani buki a London domin neman Karin agajin kudaden gudanar da wannan aiki.

XS
SM
MD
LG