Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Ma 'Yan FC Barcelona Sun San Cewa Hakan Zai Faru Watan Watarana


Da ma tun ranar da Pep Guardiola ya sanar da cewa zai yi murabus daga mukaminsa na kwach din FC Barcelona a watan Mayun 2012, magoya bayan kungiyar da yayi shekaru 4 yana jagoranci sun san cewa watan watarana, zasu fuskanci wata kungiyar dabam da yake jagoranci. Wannan rana ta zo, domin kuwa jadawalin karawar kusa da karshe ta cin kofin zakarun kulob kulob na Turai da aka fitar yau Jumma’a ya nuna cewa kungiyar Bayern Munich, wadda ke karkashin jagorancin Guardiola, zata kara da FC Barcelona, kungiyar da ya taimaka mata wajen lashe kofuna har 14, ciki har da kofin zakarun kulob na Turai guda 2, kofin Lig na Spain 3, kofin kulob-kulob na duniya 2. A dalilin irin bajimtar da yayi a FC Barcelona ma sai Bayern Munich ta dauke shi, domin ita ma yaje ya koya ma ‘yan wasanta irin wannan siddabarun nasa.

Da alamun dai Bayern Munich zata zamo zakarar Bundesliga a karshen makon nan, a karo na biyu karkashin jagorancin Guardiola, sai dai da dama sun a bayyana shakkar irin tasirin da yake da shi a kan wannan kulob da ‘yan wasanta. Har yanzu wasu bas u mance da dukar da Bayern ta sha a wasan kusa da karshe na wannan gasar zakarun kulob na Turai a hannun Real Madrid a bara ba.

Amma kuma, Hausawa sukan ce ba a san maci tuwo ba, sai miya ta kare. Idan har Bayern ta yi abin gani a karawar da zata yi da FC Barcelona, babu shakka da yawa daga cikin masu wannan shakkar zasu sauya tunani a kansa.

XS
SM
MD
LG