Javier Harnandez ne ya jefa kwallo daya rak, minti biyu tak kafin tashi daga wasa, ya taimakawa Real Madrid ta doke kishiyar ta ta tsallaken titi Atletico Madrid da kaiwa wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun kulob kulob na turai.
Hernandez ya sami damar buga wasan ne a sakamakon raunukan da ‘yan wasan Real da dama suka samu, inda a bayan wasu ‘yan kura-kuran jefa kwallo da yayi, daga baya dan wasan na gaba ya nuna cewa shi ne sinadari na ingiza zakarun na Turai zuwa ga wasan kusa da karshe a wannan karon batta da suka yia filin wasa na Santiago Bernabeu.
Hernandez, wanda aka fi sani da lakabinsa na Chicharito, ya kasance a daidai inda ya kamata domin jefa kwallon da Cristiano Ronaldo ya turo masa domin tabbatar da cewa Real ta doke ‘yan wasan Diego Simeone a karon farko tun bayan da ta lashe wannan kofi na zakarun kulob lkulob na Turai a watan Mayun bara a birnin Lisbon.
Tun daga wancan lokacin, wasanni 7 kungiyoyin biyu ke bugawa ba tare da real ta doke Atletico ba, amma rikon sakainar kashin da Atletico ta yi ma kwallon a wasan jiya, ya janyo mata faduwa, yayin da ana saura minti 14 a tashi daga wasan aka kori dan wasan ta Arda Turan daga fili.