Rundunar ‘yan Sanda ta jihar Ogun, ta cafke wani gurgu, Idris Jimoh, wanda ake zargi da addabar unguwar Matogun, a jihar da fashi da makami.
An cafke shine tare da abokin laifinsa Kamoru Anisere, bayan da mazauna unguwar suka tseguntawa ‘yan Sanda, alokacin da suka ganshi da wasu kayayyaki da suke zargin kayan sata ne, ‘yan Sanda basuyi gasa a guiwa ba wajen hanzarta cafke shi.
Cafke gurgun ke da wuya sai ya kai ‘yan Sanda, zuwa gidan abokin tu’annatin sa Kamoru, a cewar sa, amma Kamoru ya amsa cewa yasan Jimoh, amma bai taba binsa yin sata ba.
Da yake tabbatar da batun kakakin ‘yan Sandan jihar Ogun, DSP, Muyiwa Adejobi, yace da aka gudanar da bincike a gidan Idris Jimoh, (gurgu) an sami bindiga, kuma a cewar kakakin mutane biyun sun amsa cewa sun gudanar da wasu fashi a unguwar.
Ya kuma kara da cewa nan gaba za’a mika su ga rundunar ta masamman masu yaki da masu fashi da makami dake Abeokuta, domin ci gaba da bincike .