Shugaban kungiyar kwallon kafa ta tarayyar Turai, Michel Platini, ya ajiye shugabancin kungiyar a yau.
Wannan ya biyo bayan rashin nasarar daukaka karar da yayi akan hana shi duk wani mu’amula da ya shafi kwallon kafa.
Yace dalilin da yasa ya sauka daga shugabancin kungiyar shine domin ya je ya fuskanci shara’ar dala miliyan biyu da ake zargin sa dashi a kotu a Swiss.
Tun shekarar 2007, ne Platini yake shugabancin kungiyar kwallon kafa ta Turai, kafin kotun shiga Tsakani ta tabbatar da hukuncin da FIFA, ta yanke, abinda ya kawo karshe aikinsa a matsayin daya daga cikin masu fada aji a wasan kwallon kafa.
A wani jawabi bayn da kotun shiga tsakanita tabbatar da hukuncin na FIFA, Platini, yace ya kula da hukunci kotun amma wanna rashin adalci ne.