A karo na biyu kasar Brazil ta sake rufe hanyar sadarwarnan nan mai farin jini ta WhatsApp har na tsawon kwanaki uku.
Macel Montalvao alkali ne da ya umarci rufe WhatsApp har na kwanaki uku a kasar, a dalilin kin bayar da bayanai ga kotu da Kamfanin Facebook yayi akan wani bincike da gwamnati ke yi.
Wannan dai ba shine karon farko ba da WhatsApp ya shiga irin wannan hali a kasar Brazil ba. Cikin watan Disambar da ta gabata an rufe wannan kafa har ta tsawon kwanaki biyu akan irin wannan jayyaya, sai dai kuma an mayar da ita bayan kwashe awanni 12.
A wancan lokacin ne shugaban Facebook Mark Zuckerberg yace “ranar bakin ciki ce ga Brazil”
Ita dai wannan hanyar sadarwar tana da matukar farin jini a Brazil, inda aka ce kashi 90 cikin 100 na wayoyin hannu a kasar suna amfani da WhatsApp, wanda aka kiyasta cewa akwai wayoyi Miliyan 100 a kasar.
Har yanzu dai kamfanin Facebook ko WhatsApp babu wanda yayi magana kan wannan batu.
Ga cikakken rahoton.