Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gargardi Daga Asusun Kula Da Harkokin Yara Na Duniya


Asusun kula da harkokin yara na majalisar dinkin duniya ya bayyana cewa za'a iya rasa rayukan kananan yara kusan miliyan saba'in 'yan kasa da shekaru biyar da haihuwa idan gamnatoci da kungiyoyin sakai basu dauki matakan kai daukin gaggawa na cimma muradun wannan karni ba.

A rahotonta na shekara domin tunawa da kananan yara na wannan shekarar a kasar Amurka, asusun kula da hakokin yara yayi kira ga gwamnatoci da kungiyoyin bada taimako masu zaman kansu, su mayar da hankali akan kananan yaran dake cikin halin matukar bukatar taimako domin sama masu damar da zasu iya cimma burinsu na rayuwa.

A cewar babban daraktan hukumar Anthony Lake, "wadannan matsaloli da kananan yara ke fusanta suna haifar da munnan illoli a makomarsu ta rayuwa, domin zasu iya samun kawunansu cikin halaye masu matukar muni wadanda baza su yiwa kawunansu ko al'uma dadi ba. Kuma hakan zai iya durkusar da ci gaban al'uma da kuma harkokin tsaro a fadin duniya.

Ya kara da cewa yawan kwararar jama'ar da ke neman mafaka a nahiyar sunisa babban misali musamman yadda suke kara haifar da matsalolin rashin kwanciyar hankali a nahiyar.

Ya ce "rashin kyakkyawar gwamnati, da rikice-rikice, hadi da rashin iya dogaro da kai na kara ruruta wutar tashe tashen hakula wadanda ke kara tursasawa jama'a da dama barin muhallansu musamman 'yan gudun hijira daga arewacin Afirka.

Daga karshe ya ce ana iya shawo kan matsalar idan aka kara sa hannu akan inganta kananan hanyoyin zuba jari, da harkokin ilimi da kuma harkokin kwiwon lafiya a fadi duniya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG