Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati Ta Mayar Da Martani Akan Zanga Zangar Da Iyayen Yara Suka Yi A Sokoto


Da alama gwamnatin jihar Sokoto ta yi fatali da korafe korafen da iyayen yara suka yi a jihar akan bada filayen da ke jikin wata makarantar mata dake Runjin sambo a jihar domin gina shaguna wanda iyayen yaran suka ce yin hakan zai iya zama silar gurbata tarbiyar yaransu.

Iyayen yaran da suka fito suka yi zangazanga a makon daya gabata, sun nuna rashin amincewarsu ne kan matakin da gwamnatin ta dauka domin a cewarsu babu shakka gina shaguna a jikin katangar wannan makaranta zai shafi tsaro da kuma tarbiyyar dalibai ‘yan mata dake karatu a wannan makaranta.

A hirarsu da wakilin sashen Hausa na Amuryar Amurka Murtala Farouk, Alhaji Ibrahim mukaddashin shugaban kungiyar SBMC na makarantar jeka ka dawo ta Runjin Sambo ya bayyana cewa wannan makaranta dai ta mata ce, kuma ya kara da cewa tarbiyyar namiji daban take data mata, domin kuwa akwai tsauri kwarai a tarbiyyar mata.

Daga karshe ya bayyana cewa dalilin daya sa har jama’a suka kaiga yin zanga zangar kawai domin gudun yadda lamarin zai shafi tsaron da kuma tarbiyyar ‘yara mata dake karatu a wannan makaranta.

A bangaren gwamnati kuma, a wani taron manema labarai akan nasarori da ma’aikatar filaye da gidaje ta jihar, kwamishinan ma’aikatar Alhaji Bello Muhammad Abubakar Gwiwa ya mayar da martani a karo na farko inda yace iyayen yara basu fi gwamnati sanin abinda ya dace ta yi ba. Daga karshe ya ce duk wadanda suka yi korafin sun bukaci a basu shaguna ne basu samu ba.

Ga cikakkikiyar hirar anan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Direct link

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG