WASHINGTON, DC —
A yau mun sami zantawa da Bello Ibrahim wanda aka fi sani da Billy O mawaki amma fa na Hip Hop, din Hausa wanda ya shafe shekaru goma sha biyar a harkar waka.
Billy O, ya ce yana wakoki Hausa ta salon hip hop ne don ya fadakar ya kuma wa'anzantar a cewarsa da dama Malaman jamio’i, a sasshen nazarin harshen Hausa sun sha daukar wakokinsa domin yin fashin baki na kalamansa da irin darussan da ke cikin wakar tasa.
Ya kara da cewa ta dalilin waka tasa shi muamala da mutane irin karma malaman addini da farfesoshin jami’oi, wanda haka ba karamin ci gaba bane gareshi.
Ya ce burinsa shine ya samu daukakar da kudi baya iya sayanta.