Jami’an tsaro sun cafke wani matashi mai matsakaitan shekaru da yunkurin samawa tsahuwar ‘yar jarida Jamila Tamgaza wadda ta taba aiki da gidan Radion BBC hanyar arcewa daga Najeriya ta wata hanya data ratsa wani gari dake kan iyakar kasar a jihar Kwara.
Jami’an sun damke matashin mai suna Idris ne dauke da takardar Fasfo din Jamila Tangaza yayin da yayi yunkurin neman tambarin izinin tafiye tafiye na jami’an shigi da ficen kasar a wani ofishin su dake Chikanda a jihar Kwara.
Jaridar Sahara repoters ta wallafa cewa a lokacin Jamila Tangaza na zaman jira ta amshi Fasfo dinne domin ta fice daga kasarta hanyar garin dake kan iyakar kasar.
Rahotannin sun bayyana cewa Jamila ta yi batan dabo a yayin data sami labarin cafke matashin. A watan agusta daya gabata ne hukumar EFCC ta ta zargi ‘yar jaridar da yin sama da fadi akan zunzurutun kudi har miliyan dari twakas a lokacin da ta yi aiki a matsayin daraktar ma’aikatar AGIS da kuma mai ba ministan birnin tarayya shawara, Bala Mohammed.
Bayanai daga hukumar EFCC sun bayyanawa jaridar Sahara reporters cewa jami’an hukumar sun yi matukar mamakin ganin yadda tsohuwar ‘yar jaridar ta sake samun wani sabon Fasfo duk da cewa hukumar na rike da Fasfo din ta a matsayin daya daga cikin sharuddan belinta da aka bada.
Rahotanni sun bayyana cewa za’a sake damke Jamila tare da tsohon shugaban nata Bala Muhammed da zarar masu gudanar da bincike sun kammala ayyukan su.
Jiya da daddare ne hukumar EFCC ta cafke tsohon ministan Bala Muhammed akan zarginsa da yin sama da fadi akan biliyoyin kudade.