Taron masana kiwon lafiyar dan adam, da binciken zamani, sun gabatar da wata sabuwar na’ura da suka kirkira, da zata rage yawan haihuwar yara dauke da wasu dau’u’ukan cututuka. Yanzu haka dai za’a dauki wasu sinadarai a jikin duk wata mace da ke da juna biyu, da bai wuce sati biyar ba.
Za ayi amfani da sinadarin jikin mai juna biyun, wajen gano wace irin cutace zata iya kama dan tayin dake cikin ciki. Hakan zai rage irin haihuwa da akanyi a wannan zamanin da yara kanzo da wasu cututuka da ba’a san maganin suba.
Kimani nau’u’ukan cututuka sama da dubu shida 6,000 ne ake haifan yara da su, kama da ga cutar amosalin jini, da dai makamantan su, wanda akasarin su suna faruwa ne a yayin da yara ke cikin mahaifar iyayen su. Wasu daga cikin cututukan sukan haifar da kwantar da yara na tsawon lokaci a asibiti, ko kuma sukan zama sanadiyar mutuwan yaran.
Jerin masana da suka hada da Farfesa Sascha Drewlo, na jami’ar Wayne a garin Detroit jahar Michigan, sun samar da nagartacciyar hanyar da za’a bi, wajen duba jinin mahaifiya don gano irin cutar da yaro zai iya dauka, da magance hakan tun da wuri.