Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Kama Dillalin Sukari A Misira


Satin daya gabata ne wata kotu a kasar misira ta yankewa wani mai shago hukuncin daurin shekaru biyar, da kuma tarar kudi dala dubu goma sha daya, sakamakon boyewa da kin sayarwa jama’a sukari.

A cewar rahotannin, makonni kadan da suka gabata jami’an ‘yan sanda sun damke wani mutum akan hanya dauke da sukari da nayinsa ya kai kusan kilo 20, a gefen hanya suka kuma kai shi gidan yari.

Laifinsa a cewar mai shari’a shine yana sayen sukarin akan farashin gwamnati mai rangwame yana boyewa da niyyar cin riba ta hanyar sayarwa masu shaguna akan farashi mai yawa.

Kasar misira na tsakiyar fama da matsalar rashin isashshen sukari, kasar nada nau’ukan abinci iri daba daban da ake amfani da sukari, kamar su shayi da sauransu wanda rashin isashshen abin hadin wato sukari ya kawo wa jama’[ar kasar cikas.

Kamun na daga cikin matakan dakile yunkurin ‘yan kasuwa masu sayen sukarin suna boyewa domin samun riba daga baya. Gwamnatin kasar ta kirkiro da hanyar da jama’a zasu iya shiga ta yanar gizo domin yin korafi ko kai karar duk wata harkar saye da sayar da sukari ba bisa ka’ida ba.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG