Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alkawarin Rayuwa Mai Kyau Ya Rikide Karuwanci Da Karfi Da Yaji - Inji 'Yar Najeriya A Italiya


Wata matashiya ‘yar Najeriya mai suna Victoria wadda aka yi zargin dilmiyata cikin harkar karuwanci a kasar Italiya ta bayyana irin fituntunun da ta sami kanta a hannuwan wadanda suka yi fataucinta zuwa wannan kasa.

Victoria ta bada labarin yadda yadda wadanda suka yi fataucinta suka yaudareta da rayuwa tagari, da ilimin boko duk a kasar Italya amma daga karshe sai ta tsinci kanta dumu dumu cikin karuwanci.

Mujallar Daily Post ta wallafa cewa matashiyar ta bayyana haka ne a lokacin da take hira da gidan talabijin na Birtaniya a wani karamin sansanin mata ‘yan Najeriya da aka kubutar daga karuwanci a birnin Turin dake kasar ta Italiya.

Matashiyar ta bayyana cewa “bani da zabi, dole in biya shi kudin shi, tamkar ina zaman kaso ne” a cewar Victoria. Ta kuma kara da cewa mutumin da yayi fataucinta ya tursasa ta yin karuwanci domin biyan shi duk kudin da yace ya kashe yayin da yake kokarin fataucinta zuwa kasar.

Ta kara da cewa tana matukar godiya da farin ciki data sami Kanta a sansanin domin a cewarta makonni kadan da suka gabata ne ta shigo kasar Italiya ta kwalekwale ta hanyar da aka saba shigar da dubban mata daga Najeriya kasar.

Daga karshe ta bayyana cewa tafiyar da ta kwashe mil dubu biyu da dari biyar ta zama hanyar cutarwa da cin zarafi, ta ce kafin su kai kasar Libiya ta sha duka da kuma tursasata yin karuwanci domin ta biya mai fataucinta bashin da yaki karewa.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG