WASHINGTON D.C —
Majalisar dinkin duniya ta ware ranar 21 ga Nuwamban kowcce shekara tun 1996, a matsayin ranar talabijin ta duniya domin fito da muhimmanci da alfanun talabijin wajen samar da labarai a sassan duniya da dumi-duminsu.
A wannan rana ana duba irin ayyukan da gidajen talabin ke bayarwa ga alumma , da kuma jan hankalin gwamnatoci wajen tallafawa, da bunkasa gidajen talabijin, a kan haka ne muka sami zantawa da wani tsohon dan jarida kuma dan wasan kwaikwayo da yayi fice a wasan Cock Crow At Dawn Imam Usman Shehu.
Ga cikakken rahoton Baraka Bashir.