Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Matakin Da Ilimi Baya Kai Mutun, A Rayuwar Yau Da Kullun!


Sheik Jabri Sani Mai-Hula
Sheik Jabri Sani Mai-Hula

Bayan kammala yiwa kasa hidima a Abuja, Najeriya, Sheikh Jabir, ya fara aiki a matsayin malami a kwalejin Shari’a da karance karancen musulnci dake Sokoto a shekara ta 2007, kafin daga baya ya koma jami'ar jihar Sakkwato. A shekara ta 2011 Sheikh Jabir yabar Nageriya zuwa Ingila, inda yayi digirin shi na biyu, akan harkokin shari'a na gabas ta tsakiya, "LLM Islamic and Middle Eastern Studies" a Jami'ar gabacin Birtaniya.

Sheikh Jabir ya gabatar da lakcoci, Muhadarori da karance karance a jihohi daban daban a Nageriya da kasashen makwabta, harda kasar Ingila. Ya gabatar da kasidu a jami’o'i kamar su Sakkwato, Kebbi, ATBU Bauchi, Jami'ar Usmanu Dan Fodiyo, ABU Zaria da Jami'ar Nottingham a kasar ingila.

Sheikh Jabir yana gabatar da shirye shirye a Sunna TV, Africa Tv, Wisal Tv da Manara Tv. Haka kuma yana samun gayyata daga gidajen talabijin na kasa, kamarsu NTA, DITV Kaduna dadai sauran su.

Yanzu haka Sheikh Jabir yana gabatar da wani shiri mai taken RAYUWA MAI DADI a gidajen talabijin na Sunna Tv, Africa Tv3 Manara tv, WISAL Hausa da wasu gidajen talabijin da radio.

Sheikh Jabir yana karatun digirin digirgir a jami'ar Nottingham a kasar ingila. Bugu da kari, a watan maris daya wuce, an zabe shi a matsayin shugaban jama’ar musulmin dake wannan jamiar ta Nottingham, mukami ne mai girman gaske a rayuwar matasa musulmi, a ingila da musulmi masu karatu a kasar ingila. Scotland da Republic of Ireland.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG