WASHINGTON D.C —
Summayya Mohd matashiya mai aikin Sales girl, wato mai kula da kayayyaki a wani kamfanin kayan laturoni wanda aka fi sani da LG.
Matashiyar ta ce tana aikin ne domin ta zama mai dogaro da kai, bayan da ta kammala makarantar sakandire kuma bata samu damar cigaba da karatun ta ba sakamakon matsalolin yau da kullum.
Sumayya dai ta ce burin ta dai bai wuce ta karanci kwas din kimiyya ba, a yanzu rashin samun yadda ta ke so ne ta ke aikin domin ta samu ta tara kudaden shiga jami’a.
Kawo yanzu dai ta ce bata fuskanta wata matsala, kuma babban burinta ta samu damar cigaba da karatuntun gaba da sakandare.