Kimanin sama da kwayoyin cuta milliyan goma ne, kan zauna a jikin broshin wanke baki. Sau da yawa mutane kan cutar da kansu cikin rashin sani, ko mantuwa. A duk lokacin da mutun yayi amfani da broshin wankin baki, kana bai adana shi a wajen da ya kamata ba.
Kwayoyin cuta kan mamaye broshin, a cewar Suzanne Fischard, babbar likitar hakora, abu mai matukar muhimanci ga lafiya mutun itace, mutane nada bukatar sauya broshin su akai-akai, ko ace duk bayan wata uku zuwa hudu.
Idan kuma cikin kuskure mutun ya yarda broshin shi, to yana da kyau mutun ya sake broshin, kada yayi amfani da shi, don gujema daukar cuta. Mutane kan dauki wasu cututuka daga bakin su da suke zama manya cututuka a cikin jikin su.
Tsohon broshi na haddasa zaman kwayoyin cuta a bakin mutun, wankin baki a tsanake shi ke kara lafiyar baki, da kokarin wanke baki sau uku a rana. Rashin tsaftar baki kan haifar da mura, zazzabi, ciwon kai, da wasu rashin lafiya makamantan hakan.
Haka tsaftace duk wani abu da mutun zai saka a bakin shi, yana da muhimanci, kamar su cokali, tsinken sakace, da yanayin irin abincin da mutun keci, don gujema kamuwa da duk wasu abubuwa da kan iya haifar da rashin lafiyar baki.