Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Makekeiyar Tsagewar Kankara Na Zama Zuwa!


Dusar Kankara
Dusar Kankara

Masana na kara sa ido a yankin Antarctica, don ganin yadda tsibirin kankara ke neman narkewa zuwa ruwa. Ballin kanakarar da take yawo a yankin arewa maso yamma na tsibirin na Antarctica, na kokarin narkewa.

Masanan dake gudanar da bincike a yankin, sun kwashe shekaru da dama, suna bibiyar yanayin. A cewar Mr. Martin O’Leary jagoran binciken na jami’ar “Swansea” yace tun shekara ta 2010 suke lura da tsagewar kankarar.

A lokacin da suka lura cewar tsagar na kara fadada, a shekarar 2014, sun kara fahimtar cewar, kankarar tana rabewa, fiye da yadda aka saba gani. Tsagewar takai kashi tara 9% zuwa goma sha biyu 12% na baki daya girman kasar.

A watan Disamba da ya gabata dai, sun lura da karin rabewar kankarar da yakai kimanin kaso mai yawa. Tsayin tsagewar kuwa yakai nisan kilomita goma sha takwas 18. Amma ya zuwa yanzu, tsaguwar ta karu da kimanin kilomita ashirin 20, inda ta mamaye murabba’in sukwaya mita dari biya 500.

Fiye da rabin kasar Lebanon, yankin dai na hade da wani bangaren bakin teku, idan kuwa har kankarar ta nareke zatyi amfabilya cikin teku. Hakan na iya kasancewa a sanadiyar dumaman yanayi na duniya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG