Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Amazon.com Sun Kirkiri Sabuwar Kwakwalwar Zamani!


Mutun-mutumi Alexa
Mutun-mutumi Alexa

Shahararren kamfanin siye da siyarwa na yanar gizo Amazon.com, sun kaddamar da wata sabuwar hanya, da dalibai zasu iya amfani da muryoyin su don inganta ilimin su. Dalibai kan iya amfani da sabon mutunmutumin da suka kirkira mai suna “Alexa”

Dalibai na iya amfani da Alexa, wajen sanin abu da tambayoyi akan duk wani abu da ya shafi karatun su. Kana ana iya amfani da Alexa wajen rubutu ko karatu, duk wani abu da mutun ya gayama Alexa, zata rubuta shi a matsayin rubutu.

Taron farfesoshi a wasu manya-manya jami’o’I na taro don kara samar da hanyoyi da za’a inganta wannan mutun mutumin, wanda zai bama dalibai damar amfani da shi ta hanyoyi da dama. Dalibai zasu iya amfani da Alexa, wajen warware duk wasu matsalolin da suka shafi kimiyya da fasaha, a kowane mataki.

Baya ga daukar ilimi daga Alexa, mutane kan iya amfani da ita wajen sarrafa na’urorin gidajen su, kodai wajen sanyaya daki ko zafafawa. Duk wani abu da mutun ya umurci Alexa da tayi zata yi shi cikin gaggawa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG