Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Duk Shekara Kimanin Mutane Miliyan 6 Ke Mutuwa A Sanadiyyar Taba Sigari - Inji WHO


Yau kasashen duniya ke bukin tunawa da ranar yaki da shan taba sigari wacce majalisar dinkin duniya ta ware domin waiwaye kokuma tayarda jama’a daga barci domin sake jan damar yaki da shan taba sigari wacce ke haddasa illoli da dama ga lafiyar jikin dan’adam.

A wani kiyasi da majalisar dinkin duniya ta fitar ya nuna cewa kimanin mutane miliyan shidda ne ke mutuwa a duk shekara a sakamakon kamuwa da cututtukan da ke da nasaba da shan taba sigari.

Taken Bukin na bana shine hana kawa/kwalliya wajan tallace tallace na kwalayen sigari abinda hukumar lafiya ta duniya ta ce zai taimaka wajan raye shi'awar shan taba sigari a duniya a sakon ta domin bukin na bana.

Shugabar hukumar Dr Margret Chan, ta ce fatan hukumar shine ganin cewa gwamnatoci daban daban a duniya sun saka ido akan kamfanonin sigarin sun rage yadda suke kawata kwalayen sigarin yadda hakan zai rage yawan daukar hankalin jama'a musamman matasa wajan zukar taba sigari.

Kawo yanzu da likitoci sun nuna cewa taba sigari na dauke da sinadarai da yawan su ya kai kimanin dari shidda, wadanda kuma idan aka kona su zasi fitar da wasu sinadaran da yawan su ya kai kimanin dubu bakwai masu cutarwa ga bil'adama wanda kuma akasarin su ke haifar da cutar kansa ko kuma daji.

Ga cikakken rahoton.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG