A kokarin da kamfanin Facebook yake na ganin ya kawata yadda mutane zasu rika samun labarai ta kan shafinsu, yanzu haka Facebook na gwadon hanyar da mutane zasu samu labaransu cikin tsari.
Shugaban Facebook Mark Zuckerberg, yace yana son shafin Facebook ya zamanto tamkar jarida mai tsari, inda kowanne labara zai kasance cikin rukununsa.
Tun watan Oktoba kamfanin ya fara gwajin sabuwar hanyar da zata maye gurbin yadda masu amfani da shafin ke samun labaransu. Yadda kowanne labari zai kasance cikin rukununsa mai makon a gwamutse kamar yadda aka saba gani.
Babban abu mai kyau ga wannan canji da kamfanin zaiyi shine mutane zasu samu labaran da suke son gani missal idan mutum na da ra’ayin labaran wasanni ko nishadi to labaran da zasu gani kenan.