Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hattara Dai Masu Amfani Da WhatsApp


Whatsapp
Whatsapp

Rahotanni na cewa ana yiwa masu amfani da kafar sadarwa ta WhatsApp kutse, ta hanyar yaudararsu wajen sauke wata sabuwar manhaja mai suna WhatsApp Gold, sai dai kuma da zarar mutum ya amince ya sauke ta zata gurbata masa na’ura da sace masa bayanai.

Dinbim mutane sunce sun sami sako da yake basu shawarar shiga shafin yanar gizon sabuwar manhajar domin suyi rijista, sakon kuma na dauke da hanyar da zasu danna ta kaisu wannan shafi.

Masu kutsen dai na yaudarar mutane ta hanyar nuna musu abubuwan da WhatsApp Gold ke dauke da su da babu su a WhatsApp din da suke amfani da ita yanzu, inda sukace mutum zai iya aikawa da hotuna 100 a lokaci guda, kuma fitattun mutane ne ke amfani da ita amma yanzu dama ce ga duk mai so.

Da zarar mutum ya amince ya sauke manhajar nan take na’urarsa zata gurbata, ta yadda za a iya sace bayanan mutum.

Kamfanin WhatsApp na gargadin mutanen da suka sauke manhajar WhatsApp Gold a na’urarsu da su cire ta, sai dai kuma kafin su sake sauke WhatsApp din gaske dole sai sun jira kwana guda domin tabbatar da cewa na’urarsu bata da wata illa.

XS
SM
MD
LG