Kamar yadda muka saba bayan jin ra’ayoyin matasa maza da mata akan zamantakewar su da masoyan su, mukan gayyaci manya iyaye ko malamai domin bu wayar mana da kai akan wadan nan abubuwa dake ci mana tuwo a kwarya.
A yau mun sami bakuncin malama Hassana Uwa kuma dattijiya wadda ta yi mana Karin bayani akan abubuwa da kuma yadda matasan zasu lura kuma su yi la’akari da su kafin amincewa da kuma yarda da cewa soyayyar gaskiya ce.
Malamar ta nuna farin cikin ta musamman yadda matasa suka jajirce wajan tsayawa tsayin daka domin neman masoyan da suka dace da su, ta kara da cewa kawar da kwadayin duniya shine kadai zai fitar da su daga cikin wannan kunci da rudani.
Ta kara da cewa babbar matsalar samarin ita ce yadda suke tara ‘yan mata da dama kuma daga karshe su yi watsi da su. Dan haka ta ce samari da ‘yan mata aji tsoron Allah domin samun makoma mai kyau.
Ga cikakken bayanin.